
Bayan shafe shekaru goma a kasar Amurka, Laila Ali Modibbo ta dawo gida Najeriya dauke da sabuwar rayuwa da tunani na daban. Sai dai dawowar tata ba ta zo da sauki ba, domin ta iske dambaruwar boyayyun sirrikan iyali da tsohon takaddama da ya dade yana ci wa danginsu tuwo...