
"Idan har babu soyayya, to me ya kawo kishi?" Anam da Shareff sun gina katangar ƙaryata zuciyoyinsu, inda kowannensu ke tutiyar ba ya saurarar kiran ɗayan. A cikin gidan mazauna da ke cike da sarƙaƙƙiyar zamantakewa da ka'idojin iyali, sun duƙufa wajen nunawa duniya cewa tsana ce kawai ke tsakaninsu. Sai...